Mutane 130 sun mutu a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gamayyar dakarun da Saudiyya ke jagoranta ta ce ta ita ta kai harin ba.

Jami'an kiwon lafiya a Yemen sun ce kawo yanzu mutane 130 ne suka mutu a harin da aka kai a kan wasu mutane da ke bikin daurin aure.

Rahotannin farko-farko da aka fitar ranar Litinin sun nuna cewa mutane ashirin da bakwai ne suka mutu.

Jami'ai a Yemeni sun ce jiragen sama na gamayyar dakarun da Saudiyya ke yi wa jagoranci ne suka kai harin a wani kauye da ke yankin kudu mai nisa na kasar bisa kuskure.

Sai dai gamayyar dakarun ta musanta kai harin, tana mai cewa watakila 'yan ta'adda ne suka kai shi.

Gamayyar dakarun -- wacce ke goyon bayan gwamnatin Yemen -- ta kwashe watanni tana kai hari a kan mayakan da ke goyon bayan 'yan tawayen Houthi.