'A dawo mana da mahajjata da suka mutu'

Image caption Shugaban addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamene'i.

Shugaban addini a Iran, Ayatollah Ali Khamene'i ya gargadi kasar Saudiyya da cewa za ta fuskanci bacin ran kasar idan har ba ta dawo da gawarwakin 'yan kasar Iran din da suka mutu sakamakon turmutsutsu a kan hanyar zuwa wurin jifan shaidan.

A wani jawabin sa da aka wallafa a shafin intanet, Ayatollah Khamene'i ya zargi kasar Saudiyya da sakaci wurin daukar alhaki da kuma kumbiya-kumbiya game da lamarin.

A ranar Lahadi ne shugaban addinin ya bukaci birnin Riyadh da ya nemi afuwa dangane da abin da ya faru, duk da cewar Sarkin Saudiyya ya bayar da umurnin sake duba tsarin matakan kula da lafiya.

A ranar arfa ne dai mutane sama da 800 suka rasa rayukan su, cikin su har da 'yan kasar Iran sama 140, lamarin da wasu ke cewa shi ne mafi muni a tsawon shekaru 25.