An daga tutar Palasdinawa a Majalisar dinikin Duniya

Tutar Palasdinawa a MDD Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya ce mutanan sa ba za su ci gaba da aiki da yarjeniyoyin da suka sa hannu da Isra'il ba.

Da yake jawabi a wajan taron Majalisar Dinikin Duniya, ya zargi Isra'ilawa da ci gaba da saba yarjeniyoyin da aka fi sani da Oslo Accords da aka sawa hannu a shekarar 1993.

Masu lura da al-amura sun ce jawabin Shugaba Abbas wata alama ce da ke gargadin cewa gwamnatinsa na iya dakatar da duk hadin kan da suke ba Isra'ila ---- inda za su barta ta dauki cikakken nauyin dukkan yankunan da ta mamaye.

Bayan jawabin na sa, Shugaba Abbas ya halarci wani biki mai cike da tarihi inda a karon farko aka daga tutar Palasdinu a hedilkwatar MDD.

Sakataren MDD, Ban Ki Moon ya ce wannan wata rana ce ta alfahari ga Palasdinawa a duk fadin duniya.