Ana zargin PHCN da tsawwala kudin lantarki

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu amfani da wutar lantarki na zargin kamfanoni rarraba wutar da tsuga masu kudi fiye da kima.

Masu amfani da wutar lantarki a Nigeria na zargin kamfanonin rarraba wutar da tsuga masu kudi fiye da kima.

Lamarin ya sa masu amfani da shi yin dafifi a ofishin kamfanin da ke Bauchi, domin mika korafin su.

Hakan na zuwa ne a yayin da bayanai suka nuna cewar ana samun ingantacciyar wutar lantarki a yanzu fiye da in an kwatanta da baya a fadin kasar.

Mutanen suna zargin cewa a wasu lokuta ma'aikatan kamfanin lantarki na cajinsu kudi ba tare da duba mitar ba, ko ma su yanke wutar baki daya.

Matsalar wutar lantarki dai na daya daga cikin matsalolin da suka dade suna ci wa Najeriya tuwo a kwarya da kuma nakasa tattalin arzikin ta.

Hukumomin kasar dai sun ce adadin wutar lantarkin da ake samar wa ya karu fiye da da, tun daga rantsar da sabuwar gwamnati.