Amurka ta sanya wa IS takunkumin kudi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu daga cikin jagororin kungiyar IS

Amurka ta sanar da sanya takunkumin harkokin kudi a kan manyan jagororin kungiyar IS su fiye da talatin tare da abokan huldarsu da sauran kungiyoyi makamantansu.

Hakan na daga cikin yunkurin hana su yin amfani da hanyoyin harkokin kudade na duniya.

Mutanen da aka dauki matakin a kan su sun fito ne daga kasashen Rasha da Faransa da kuma Biritaniya.

Sanarwar, wacce aka fitar a Washington babban birnin Amurka, ta zo a dai-dai lokacin da ake taron Majalisar Dinkin Duniya don fadada yakin da ake yi da ta'addanci wanda shugaba Obama ke jagoranta.