Gwamnatin Afghanistan ta kwato Kunduz

Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin Afghanistan ta ce ta kwace iko da garin Kunduz da ke arewacin kasar daga hannun mayakan kungiyar Taliban.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida Sediq Sediqqi ya wallafa a shafin Twitter cewa, a halin yanzu ana kawadda sauran mayakan Taliban daga garin wadanda suka rasa mutane da dama.

Babu wani martani daga kungiyar Taliban din da mayakan ta suka yi ta kurarin ci gaba da rike iko da garin bayan da suka mamaye a ranar Litini.

Garin Kunduz dai shi ne babban birni na farko da ke tsakiyar kasar da ya fada hannun mayakan Taliban tun bayan da Amurka ta jagoranci hambarad da su daga mulki shekaru goma sha hudu da suka gabata.