'Boko Haram babbar barazana ce '

Jagoran kungiyar Boko Haram
Image caption Jagoran kungiyar Boko Haram

Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Amnesty International ta bayyana cewar har yanzu kungiyar Boko Haram babbar barazana ce, duk kuwa da matakan da sojoji suke dauka akan kungiyar.

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ta fitar a jiya, inda ta ce kungiyar ta kashe fararen hula 1,600 a watanni hudun da suka gabata.

Amnesty International ta ce matakin da sojoji ke dauka da hare- haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a Najeriya da kamaru da Chadi da Niger sun yi sanadiyar rayuka akalla 1600 tun farkon watan Yuni.

Amnesty ta ce don haka ya zama dole kasashen da wannan lamari ya shafa, su dauki dukkanin matakan da ya kamata domin tabbatar da da tsaron lafiyar fararen hular da wannan al'amari ya shafa

Kungiyar Amnesty ta kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike game da mutanen da jami'an tsaro suka musgunawa.kansa wanda kuma babu son kai a ckinsa game da laifukan da aka tafka a wannan tashin hankali a Kamaru