Dole yan Najeriya mu sauya hallayar mu- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan batutuwa da dama a jawabin da ya gabatar wa alummar kasar da safiyar Alhamis a bikin cikar Najeriya shekaru 55 da samun yancin kai daga turawan mulkin malaka.

Shugaba Buhari ya yi bayani a kan dalilan da suka sa bai tura sunayen mutanen da yake son ya nada a matsayin ministoci ga Majalisar datawan Najeriya da wuri ba.

Shugaba Buhari ya dai dora alhaki jinkirin da aka samu wajen samun sunayen minitocin ne kan yanayin yadda tsohuwar gwamnati ta Goodluck Jonathan ta mika masu harkokin mulki.

Ya kuma kara da cewa har yanzu bai gama mika sunayen wadanda ya ke son ya nada a matsayin ministoci gabadaya ga majalisar dokoki ta tarayya ba amma ya ce zai kamala yin haka nan gaba.

Game da tarin matsalolin da gwamnatinsa ta gada kuwa shugaba Buhari ya ce sun ga yadda aka yi tabargaza da almubazzaranci da tarin dukiyar kasa a 'yan shekarun da suka gabata kuma gwamnatinsa ta APC tana kokarin bulo da tsare tsare na magance irin illolin da wannan tabargaza ta haifar.

A cewar sa a matakin farko gwamtin tarayya ta shawo kan matsalar tarin albashi ma'aikata da ke kan wasu jihohi wanda ba don haka ba da lamarin zai iya tayar da hatsaniya.

Sai dai shugaba Buhari ya kara da cewa idan ana son aga sauyi mai muhimanci da ma'ana dole ne 'yan Najeriya su sauya dabiarsu ta zama kara zube da kuma rashin bin doka da kaida.