An kashe mutane 10 a kwaleji a Amurka

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Kwalejin da aka yi kisan a Amurka

'Yan sanda a jihar Oregon ta Amurka sun ce an yi harbe-harben kan mai uwa da wabi a wata kwaleji, inda aka kashe mutane akalla 10.

Lamarin ya janyo jikkatar wasu fiye da 20.

Rahotanni sun ce an tsare wanda ya kai harin a kan wata karamar kwalejin ilimi mai zurfi da ke birnin Roseberg.

'Yan sanda na bi aji-aji suna bincike a ginin makarantar.