'Yan Boko Haram 80 sun miƙa wuya a Bama

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption 'Yan Boko Haram 80 da kwamandojin su sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Rundunar sojin Nigeria ta nanata cewa tana samun galaba a yakin da ta ke yi da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

A cewar rundunar, yanzu haka akwai wasu mayakan Boko Haram din 80 da suka mika wuya ga sojojin kasar a garin Bama da ke jihar Borno.

Sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce cikin wadanda suka mika wuya har da wasu kwamandojin kungiyar, da masu samar musu da abinci da kuma wasu wadanda dasu ne aka kaddamar da hare- haren ta'addanci a garin Baman da ke jihar Borno.

Rundunar ta ce 'yan Boko Haram din sun mika kan su ne a ranar Alhamis sakamakon farmakin da sojojin ke kai musu ba kakkautawa.

A cikin makon da ya gabata ma wasu 'yan Boko Haram 200 sun mika wuya a garin Banki da ke kan iyaka da kasar Kamaru, kamar yadda sojojin Nigeria suka yi ikirari.

'Yan Nigeria da dama za su so gani a zahiri a kan cewar ko tabbas mutanen da suka mika wuya 'yan Boko Haram ne, ba wai fararen hula bane wadanda 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su.