An bada belin Diezani Alison-Madueke

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Diezani na da karfin fada a ji a gwamnatin Jonathan

Rahotanni daga London sun ce, an bada belin tsohuwar ministar harkokin man fetur ta Nigeria, Misis Diezani Alison-Madueke da aka kama yau.

Amma za ta kai kanta ofishin 'yan sanda dake Charing Cross a London ranar Litinin mai zuwa.

Hukumar kula da laifuka ta Birtania ta wallafa a shafinta na intanet cewar "sashin yaki da rashawa da ba'a dade da kafawa ba, ya kama wasu mutane biyar a London a cikin wani bincike da ake yi kan zargin cin hanci da kuma halatta kudaden haram."

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta yaki cin hanci da rashawa musamman a bangaren man fetur na kasar, inda tuni ya bayyana cewar gwamnatinsa na samun bayanai akan kudaden da aka sata a ma'aikatar Man fetur ta kasar, kuma nan bada dadewa ba za a fara hukunta wadanda ake zargi.

Rahotanni sun ce tun gabanin a rantsar da Shugaba Buhari, Misis Alison-Madueke ta fice daga kasar zuwa kasashen waje.