'Yan kunar-bakin-wake sun kashe mutane 14 a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu mata 'yan harin kurnar bakin-wake su hudu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun tayar da bam da ke jikinsu daya bayan daya a unguwar Sajeri da ke birnin Maiduguri a ranar Alhamis.

Wata sanarwar da kakakin rundunar, Kanal Sani Kukasheka Usman ya aikewa BBC ta ce uku daga cikin 'yan ta'addan sun tayar da bam dinsu ne a unguwa daya, yayin da ta hudu ta tayar da nata a gaban wani masallaci.

Kanal Usman ya ce ya zuwa yanzu mutane akalla 14 ne suka rasa rayukansu -- ciki har da 'yan kurnar-bakin-waken yayin da mutane 39 suka jikkata.

Ya yi kira ga mutane -- musamman wadanda ke zama a wuraren da lamarin ya faru --da su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke wakana a kewayensu, yana mai cewa soji suna yin duk abin da kamata domin tabbatar musu da tsaro.

Sanarwar ta ce abu ne mai muhimanci a tabbatawar wa al'ummar yankin da cewa duk da kokarin da mayakan kungiyar Boko Haram suke yi wajen mayar da hannu agogo baya a ci gaban da ake samu wajen dawo da zaman lafiya da kuma tsaro a cikin kasar, ba za su yi nasara ba.