Alhazan Nigeria da suka rasu sun kai 74

Image caption Har yanzu akwai alhazan Nigeria a asibiti

Hukumar aikin hajji ta Nigeria ta ce a yanzu adadin 'yan kasar da suka rasu a turmutsitsin da ya faru ranar Idi ya kai 74.

Shugaban hukumar Alhaji Abdullahi Mukhtar Mohammed ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da BBC.

A cewarsa, alhazai daga jihohi wadanda suka rasu su 54 ne sai kuma na kamfanoni masu zaman kansu mutane 20.

"Wadanda suka jikkata sun kai mutane 75 kuma har yanzu ba a ji duriyar mutane 243 ba," in ji Mohammed.

Shugaban hukumar alhazan ya kara cewa jihar Sakkwato ita ce tafi yawan adadin wadanda suka rasu a Muna a hanyar zuwa jifan shaidan.