Mutane 26 sun mutu a Guatemala

Hakkin mallakar hoto focusbangla
Image caption Zezayar Kasa

Masu aikin ceto a Guatemala na ci gaba da tono laka da duwatsun da suka rufta a wani kauye da ke kusa da babban birnin kasar domin gano daruruwan mutanen da suka bace sakamakon zezayar kasa.

Wannan lamari ya kasance daya daga cikin abu mafi muni da kasar ta fuskanta a cikin shekaru da dama in da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar zezayar kasar da ta shafi gidaje kana suka rufta a kauyen El Cambray Dos wanda ke da nisan kilomita 15 daga gabashin birnin Guatemala.

Masu aikin ceton sun ce akalla mutane 26 sun mutu.

'Yan jaridar da ke wajen sun ce mutanen da suka rufta sakamakon zezayar kasar na ta kira tare da tura sakonnin karta kwana na salula domin a kawo musu dauki.