Hajji: Nigeria ta gabatar da korafi

Image caption Alhazan Najeriya

A yayin da ake ci gaba da samun karin alkaluman alhazan Nigeria da suka mutu a turmutsutsin da ya faru a kan hanyar zuwa jifa a Mina da ke kasar Saudi Arabia , hukumomin aikin hajjin Nijeriya sun ce sun gabatar da wasu korafe-korafe ga hukumomin kasar Saudia kan wasu batutuwa dangane da hatsarin.

Hukumar aikin hajjin ta Nijeriya ta ce a wani zama da aka yi, Nijeriya ta gabatar da korafe-korafe kan abin da ya shafi aikin hajji da kuma gaggauta neman samar da bayani kan adadin 'yan Nigeria da suka mutu a hadarin na ranar sallah.

Hukumar aikin hajji ta Nijeriyar da kuma jagoran alhazan kasar Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu sun tabbatar da cewa sun gana da ministocin Saudia masu kula da aikin hajji a wasu zama da su ka yi har sau biyu, in da su ka gabatar da wasu bukatu na Nijeriya kan abin da ya shafi aikin hajjin musamman ma batun 'yan kasar da hadarin turmutsutsun Mina ya rutsa da su.

Shugaban tawagar mahajjatan Nigeria a aikin hajjin na bana kuma Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na biyu ya yi wa alhazai Karin bayani kan bukatun da suka mikawa ministocin na aikin Hajjin Saudia.

Alkaluman baya bayannan dai na nuna cewa alhazan Nigeria 74 ne kawo yanzu hukumomi suka tabbatar sun mutu sakamakon turmutsutsun da aka yi ranar Sallah a Mina, wasu 75 kuma suka jikkata, sannan ake neman wasu 243 kuma da har yanzu ba a ji duriyar su ba.