Za a karrama Ali Nuhu

Image caption Ali Nuhu ya yi fice a shirin fina-finan Kanywood da kuma Nollywood wandan da ake yi a arewaci da kuma kudancin Najeriya

Jaridar Leadership a Najeriya za ta karrama Ali Nuhu a matsayin gwarzonta na shekarar 2014 a cikin jerin wadanda za ta karrama a bikin bayar da kyaututtuka na Leadership Awards da ta saba yi a duk shekara.

A cikin sanarwar da jaridar ta buga a wasu shafuka na musamman, ta ke kuma bugawa a cikin jaridar a kullum, jaridar ta ce jarumi Ali Nuhu shi ne zabin jami'an hukumar gudanarwa na kamfanin a matsayin gwarzon dan wasa na shekarar 2014.

Cikin dalilan da suka sa Ali Nuhu ya kai wannan matsayi sun hada da yin fice a yin shirin fina-finan Hausa watau Kannywood wadan da ake yi a arewacin kasar da kuma Nollywood wadanda ake yi a kudancin kasar da harshen turanci, wanda a kowannen su ya taka muhimmiyar rawa ta a zo a gani har ya samu kyaututtuka.

Sanarwar ta ce jarumin ya fito a fina-finai sama da 165 na Hausa da kuma kalla fina-finai 65 na harshen Turanci.

Haka nan kuma jarumin ya zamo jakadan wasu manyan kamfanoni a cikin kasar.

An haifi Ali Nuhu a ranar 15 ga watan Maris 1974. Mahaifinsa mutumin Balanga ne a jihar Gombe, mahifiyarsa kuma daga Bama a jihar Borno. Ya girma a Jos jihar Plateau, sannan ya yi karatu a jami'ar Jos a inda ya samu digiri a fannin nazarin kasa watau Geography.