Ambaliya ta kashe mutane 16 a Faransa

Hakkin mallakar hoto b
Image caption A ranar Asabar da daddare ne aka yi ruwa tamkar da bakin kwarya da ya jawo ambaliyar.

Kimanin mutane 16 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa, bayan ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya, a kudu-maso-gabashin Faransa.

Masu ceto suna neman wadanda har yanzu ba a gan su ba.

A birnin Canne na Faransa, ambaliyar ta dora wasu motoci kan wasu a kan tituna, an kuma tura 'yan-sanda don kare birnin daga masu kwasar ganima.

Firai ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce hukumomi za su yi iya kokarinsu wajen agaza wa wadanda lamarin ya shafa.

Ya ce, "Da sunan gwamnatin Faransa, ina son tabbatar da goyon bayanmu ga iyalan wadanda lamarin ya shafa. Wannan bala'i wata jarrabawa ce ga Faransa."

Shi ma shugaban kasar Francois Hollande, ya kai ziyara wajen da lamarin ya afku don gane wa idanunsa yawan barnar da ambaliyar ta yi.