Ana rikicin siyasa a Guinea

Hakkin mallakar hoto
Image caption Alpha Conde da abokin adawar sa Cellu Dalein Diallo

Ana rikici tsakanin gwamnati da kuma magoya bayan 'yan adawa a Guinea yayin da ya rage saura kwanaki a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar a ranar 11 ga watan da muke ciki.

Fada ya barke ne a birni na biyu mafi girma a kasar wato N'Zerekore a ranar jum'ar da ta gabata kafin shugaba Alpha Conde ya kai ziyara birnin domin yakin neman zabe.

Magoya bayan sa sun fusata magoya bayan babban dan adawar sa Cellu Dalein Diallo bayan da su ka ce wa masu shaguna su rufe shagunan su.

Rikicin ya ci gaba har zuwa ranar asabar.

Jami'ai a asibiti sun ce akalla mutane shida sun samu raunuka, yayin da wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya ce mutum guda ya rasa ran sa.