Harin bam ya kashe mutane 10 a Nijar

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a kasashen da ke yankin tafkin Chadi.
Bayanan hoto,

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a kasashen da ke yankin tafkin Chadi.

A kalla mutane goma ne suka mutu a wani hari da 'yan kunar bakin wake su hudu suka kai ranar Lahadi da safe a garin Difa na Jamhuriyar Nijar.

Hukumomi a jihar sun ce wadanda suka mutun sun hada da soja daya da farar hula biyar da kuma 'yan kunar bakin waken hudu.

Harin farko dai bam din ya tashi ne kusa da wani kanti sai na biyu wanda ya tashi a kusa da barikin rundunar tsaro yayin da dan kunar bakin wake na karshe ya sulale.

Ana zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram ne suka kai wannan hari, wanda shi ne na uku da kungiyar ta kai a yankin na Difa a cikin mako guda.