Kotu ta samu izinin binciken Diezani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan London za su yi wa Diezani tambayoyi

Hukumar binciken manyan laifuka ta Birtaniya NCA ta samu amincewar kotu domin ta ci gaba da binciken Diezani Alison-Madueke tsohuwar ministar mai ta Nigeria.

Hukumar ta gabatar da wannan bukatar ga kotun majistire ta Westminster da ke London a ranar Talata.

Hakan zai baiwa hukumar damar ci gaba da rike wasu kudade da ta kwace daga gidan tsohuwar ministar yayin bincike, kuma zai ba su damar ci gaba da gudanar da bincike a kanta.

Rahotanni na cewa, sauran mutane hudu da ake zargi tare da Diezani suna ci gaba da fuskantar bincike.

Hukumar ta wallafa a shafinta na intanet cewar "sashen yaki da rashawa da ba'a dade da kafawa ba, ya kama wasu mutane biyar a London a cikin wani bincike da ake yi kan zargin cin hanci da kuma halatta kudaden haram."

A shekarar 2014 ne, tsohon shugaban babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi, ya zargi babban kamfanin man fetur na Najeriya, wanda Diezani ke shugabanta, da kin saka biliyoyin daloli a asusun bankin kamar yadda dokar kasar ta bayar da umarni.

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta yaki cin hanci da rashawa musamman a bangaren man fetur na kasar, inda tuni ya bayyana cewar gwamnatinsa na samun bayanai akan kudaden da aka sata a ma'aikatar man fetur ta kasar, kuma nan bada dadewa ba za a fara hukunta wadanda ake zargi.

Rahotanni sun ce tun gabanin a rantsar da Shugaba Buhari, Misis Alison-Madueke ta fice daga kasar zuwa kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto Google