Medicins Sans Frontieres ta bukaci ayi bincike

Hakkin mallakar hoto MSF
Image caption Harin da aka kai asibiti a Kunduz

Kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontieres ta bukaci a yi bincike mai zaman kansa na kasa da kasa dangane da hare-haren da aka kai wa asibitinta a Kunduz da ke Afghanistan wanda ta dora alhakinsa a kan sojojin Amurka.

Kungiyar ta ce harin wanda ya kashe ma'aikatanta goma sha biyu da majinyata goma, a fili laifin yaki ne, kuma ba za ta iya dogara a kan binciken Amurika ba.

Sojojin Amurka sun ce sun kai hari ta sama ne a kewayen asibitin kan 'yan tawayen Taliban, wadan da ke harbi kai tsaye a kan sojin Amurka, bayanin da kungiyar ta yi watsi da shi .

Kungiyar ta ce harin da aka kai ya yi raga-raga da asibitin ta yadda ba zai moru ba dan haka ta janye daga Kunduz.

Sakataren harkokin tsaron Amurka Ash Carter ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike akan harin.