IS ta rusa gini mai tarihi a Palmyra

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wurin tarihi a Palmyra

Mayakan IS sun ruguza wani gini mai siffar kofar shiga gari da shekarunsa ya kai kimanin 2000 a birnin Palmyra.

Ginin da aka yiwa lakabi da Arc of triumph ya kasance an gina shi tun a karni na biyu, kuma ana kyautata zaton an gina shi ne domin murnar samun nasarar da Rumawa su ka yi a wancan karnin.

Bayanin rushe wannan wuri mai tsohon tarihi ya fito ne daga bakin wasu jami'ai daga yankin.

Wata kungiya mai lura da al'muran da ke faruwa a Syriya wacce ke London, ta ce bayanan da ta ke samu ya tabbatar da rusa wannan gini na tarihi.

A hirar da yayi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kula da adana kayan tarihi na Syriya Ma'amoun Abdulkarim ya tabbatar da faruwar hakan, sannan ya kara da cewa muddin Palmyra na karkashin ikon IS, to birnin mai tsohon tarihi zai iya lalacewa.

Mayakan IS sun kame wuraren tarihin na Palmyra ne daga hannun sojojin gwamnatin Syria a watan Mayu a in da su ka shiga ruguza wasu kayyakin tarihin da kuma gine-ginen da ke cikinsa.