An damke 'masu hada baki' da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Mutanen da ake zargi da hannu a Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta damke mutane uku da take zargin su da hada baki da kungiyar Boko Haram.

Rundunar ta ce nasarar kamen da ta yi, ya biyo bayan tsare Mohammed Maina wanda ta bayyana shi a matsayin mai daukar dawainiyar Boko Haram da kuma samar wa kungiyar kwayoyi.

Sanarwar da kakakin sojin, Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar, ta ce mutane ukun su ne; Jikana Alhaji Goni dan shekaru 29, da Alhaji Musa Alhaji Modu dan shekaru 37, da kuma Alhaji Aba'ana Na Alhaji Sule dan shekaru 40, kuma dukansu 'yan unguwar Hausari ne a Maiduguri.

Sanarwar ta ce mutane ukun suna ba da bayanai masu mahimmanci kan yadda za a samu nasara a kan Boko Haram.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin na rundunar sojin Nigeria din.