Boko Haram ta kashe sojin Chadi 11

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Chadi sun ce an kashe dakarunsu 17.

Rahotanni daga kasar Chadi na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin kasar 11, yayin da suka jikkata soji 13 a wani hari da suka kai musu.

Kamfanin dillacin labaran AFP ya ce jami'an tsaron kasar sun tabbatar da kai kashe sojojin a harin da aka kai musu a kusa da Tafkin Chadi, kusa da kan iyakar kasar da Najeriya.

Ya kara da cewa an kashe sojojin kasar guda goma sha bakwai.

Sojojin suna cikin sojojin rundunar hadin gwiwa da kasashe biyar na yankin takfin Chadi suka kafa domin yakar kungiyar ta Boko Haram.