Ciwon Sukari a lokacin ciki: Ya sa na sauya rayuwata

Image caption Shaida Akbar mai yara hudu tare da 'yar karamar 'yar ta

Shaida Akbar, kamar yadda dubban mata masu juna biyu ke kamuwa da cutar a duk shekara, ta kamu da wani nau'i na ciwon sukari da mata ke kamuwa da ita, a lokacin da take dauke da juna biyu tana da shekaru 24.

A cewar kungiyar agaji ta masu ciwon sukar da ke Ingila watau Diabetes UK, sinadarin da ke bulowa idan mace tana da ciki, suna hana sinadarin insulin daga kula da yawan sukarin da ke cikin jini daidai.

A yanzu kungiyar agajin ta na gargadin mata su tabbatar cewa kibarsu bata wuce daidai misali ba, wanda ta ce shi ne muhimmin abin da za su iya yi domin rage yiwuwar kamuwa da cutar.

"A lokacin da likita ya gaya min ina da cutar sukari a lokacin da na ke da juna biyu, na kadu amma kuma sai na gayawa kaina cewar dole na canza wasi dabi'u na," in ji Shahida.

A cewar hukumar inshorar lafiya ta Ingila, mutane 18 a cikin mata 100 da suke haihuwa a Ingila da kuma Wales, ciwon zai iya shafarsu.

Ba a ko da yaushe yake bayyana alamomi ba, amma kuma yawan fitsari da yawan gajiya suna daya daga cikin alamomin yawan sukari a jinin mutum.

Shaida ta ce "An fi ganin cewar iyalai 'yan kasar Asiya idan suna da kiba, an fi ganin yiwuwar kamuwa da cutar gare ka."

Likitoci za su iya ba da shawarar a kan yanayin cin abinci da kuma rayuwa ko kuma ka yi maganin cutar ta hanyar shan magunguna ko allurar insulin.

Idan har ba a magance cutar ba, to yanayin zai iya zama hadari ga lafiyar mahaifiyar da, dan da ke cikinta, wanda hakan zai iya jawo yiwuwar a haifi jariri da nakasa, ko a haifi jariri wanda nauyin shi ya wuce yadda ya kamata kuma sai dai a yi tiyatar gaggawa a ciro jaririn. Akwai kuma yuwar zubar cikin.

Image caption Yadda jiki ke kayyade sukarin da ke cikin jini

Libby Dowling wani babban mai ba da shawara kan cutar sukari, ya ce "Ya kamata mace mai ciki ta yawaita ganin ungozoma idan har ta kamu da wannan cutar."

A lokuta da dama, yanayin sukarin jikin mutum zai iya dawowa daidai bayan mace ta haife jaririn.

Amma kuma masu bincike a hukumar agaji ta ciwon sukari a Biritaniya sun ce idan har mace ta kamu da ciwon sukari a lokacin da take da juna biyu, yana iya kara yiwuwar kamuwa da wani irin ciwon suga wanda ake kira diabete na 2.

Haka lamarin ya faru da shaida wacce yanzu ta shiga cikin shekarunta na 40 a rayuwa.

'Canjin Rayuwa'

"Kamuwa da cutar sukari ya canza min rayuwa," in ji Shaida.

"Da sai na yi zama na a gida, a da an damu da atisaye ba".

"Amma kuma bayan na gano cutar da na ke tare da ita, sai na rage yawan ciye ciye da cin shinkafa."

Cutar sukari na diabetes 2 ta fa zama ruwan dare a 'yan kudancin Asiya kuma zai iya jawo cututuka kamar su ciwon zuciya idan har ba a kula da shi ba.

Idan mahaifiya tana da cutar sukari a lokacin da ta ke da juna biyu, da ita da 'ya'yan ta sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar sukari ta diabete 2 daga baya.