IMF ta yi hasashen tattalin arzikin Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar IMF, Cristen Lagarde

Hukumar lamuni ta duniya, IMF ta yi hasashen cewa ba za a samu bunkasar tattalin arziki ba a kasashen Afrika kudu da hamadar, kamar yadda aka yi hasashe tun da farko a bana.

A sabon rahotonta, hukumar ta IMF ta ce ci gaban da za a samu zai yi kasa daga kashi biyar zai koma kashi 3.8.

An samu koma baya din ne sakamakon rashin siyo kayayyaki daga China wacce ita ce babbar abokiyar kasuwancin kasashen nahiyar.

Daga cikin hasashen na IMF a kasashen Afrika akwai:

  • Nigeria za ta samu bukansa kashi hudu daga kashi 6.25 a shekarar 2014
  • Angola za ta bunkasa kashi 3.5 daga kashi 5 a shekarar 2014
  • Afrika ta Kudu za ta bunkasa kashi 1.4 daga kashi 1.5 a shekarar 2014
  • Ghana za ta bunkasa kashi 3.5 daga kashi 4 a shekarar 2014
  • Ethiopia za ta bunkasa kashi 8.7 daga kashi 10.3 a shekarar 2014