IS ta kai hari Basra da ke Iraqi

Hakkin mallakar hoto ISLAMIC STATE
Image caption IS ta kai hari kusa da Basra da ke Iraqi

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta IS ta ce ta kai harin bam a kusa da birnin Basra da ke kudancin Iraqi in da mutane goma su ka mutu.

A cikin wani sako da su ka wallafa a shafin sada zumunta na intanet, kungiyar ta ce dakarunta sun dana bam ne a cikin wata mota a wajen da 'yan shi'a su ke taruwa.

Kungiyar IS dai na rike da ikon mafi yawa daga cikin garuruwan da ke arewacin Iraqi.

A wani labarin kuma mutane akalla arba'in sun mutu sakamakon wasu hare-hare da aka kai a jiya litinin a lardin Diyala da ke gabashin kasar ta Iraqi, yayin da wasu mutanen goma sha uku kuma su ka mutu a harin da aka kai Bagadaza.