'Yan gudun hijira: Turai ta fara yi wa tufka hanci

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jiragen ruwan za su rika kama kanana jirage da kwale-kwalen da ke dauke da 'yan ci-rani.

Wasu jiragen ruwa na yaki guda shida daga kasashen Tarayyar Turai za su fara kama kananan jiragen ruwa da kwale-kwale masu dauke da 'yan gudun hijra a tekun Bahar-Rum.

Manyan jiragen ruwan dai za su yi sintiri ne a kan tekun da ya hada kasashen duniya, karkashin jagorancin wani babban sojan ruwan kasar Italiya.

Wannan dai shi ne sabon yunkurin Tarayyar Turai na hana 'yan ci-rani masu kaura zuwa yankin.

Kawo yanzu dai masu gudun hijra daga Syria sama da dubu 130 ne suka ketara zuwa kasar Rum daga Libya.

Sai dai duk da haka ana samun karin 'yan gudun hijira daga Syria wadanda ke tserewa yakin basarar da ake yi a kasar, inda suke bi ta hanyoyi da dama zuwa Turkiya, kafin su ketara Turai.