Bincike kan harin da Amurka ta kai Kunduz

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption MSF ta ce kai hari a kan asibinta tamkar aikata laifukan yaki ne.

Kungiyar likitoci ta na-gari na-kowa, Medecins Sans Frontieres, MSF ta ce za ta gudanar da bincike a kan harin da jiragen Amurka suka kai kan asibitin birnin Kunduz na kasar Afghanistan.

Kungiyar ta ce ba ta amince da aniyar sojoji ta gudanar da bincike kan harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 22 ba.

MSF za ta yi binciken ne a karkashin dokar kasashen duniya wacce ake kira Geneva Convention da aka kafa a shekarar 1991.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da ake yunkurin fitar da 'yan kungiyar Taliban daga birnin na Kunduz.

MSF ta ce an tsara harin da aka kai a birnin don haka, a ganin ta, ba hari ne da aka kai bisa kuskure ba.

Ta kara da cewa kai harin tamkar aikata laifukan yaki ne.