Majalisa za ta zauna kan ministocin Buhari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bukola Saraki ya ce ba zai bude takardar da ke dauke da sunayen ministocin ba sai a zauren majalisar.

A ranar Talata ne 'yan Majalisar Dattawan Najeriya za su koma bakin aiki, a karon farko tun bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aikewa shugaban Majalisar sunayen mutanen da yake son nadawa a mukaman ministoci.

A makon jiya ne Shugaba Buhari ya aika da sunayen, kuma shugaban Majalisar Dattawan, Bukola Saraki, ya ce za su fara tantance ministocin da zarar an aiko musu da sunayen su.

Kafafen watsa labaran kasar dai sun yi ta yin shaci-fadi game da sunayen da aka aikewa Majaliasar, sai dai shugaban Majaliasar ya ce ba zai bude takardar da aka rubuta sunayen ministocin ba sai a zauren Majalisar.

'Yan kasar sun kwashe tsawon lokaci suna jira Shugaba Buhari ya bayyana ministocinsa, tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun da ya gabata.