Syria: An gargadi kasashen Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria masu san tsallakawa Turai

Kasar Turkiyya ta gargadi Tarayyar Turai cewa karin 'yan gudun hijirar kasar Syria miliyan uku ka iya gudu daga kasar a yayin da yakin basasar kasar ke ci gaba da kamari.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk, wanda ya bayyana hakan ga 'yan majasar Turai, ya kara da cewa sun samu wadannan alkaluman ne daga wajen shugaban Turkiyya Receb Tayyip.

Ya ce "A lokacin da na ziyarci yankin, duk mutanen da na tattauna da su; daga shugabannin kasa zuwa 'yan gudun hijira da ke sansanoni, a Turkiya da Jordan, ko Masar, sun yi min gagadi a kan abu guda."

"Idan har Assad ya yi nasarar ci gaba da mulki, to fa za a samu karin mutanen da ke yin gudun hijira daga kasar," in ji Tusk.