'Yan Boko Haram sun fice daga Gaidam

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shekau da wasu mayakan Boko Haram

Rahotanni daga garin Gaidam a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun fice daga garin bayan da suka kwashe abinci daga wasu shaguna.

Rahotannin sun ce babu wani da ya rasa ransa a harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai da yammacin ranar Laraba.

Sai dai rahotannin sun ce mayakan sun kona wasu shaguna bayan da suka debi ganima kuma sun tafi da wasu motocin soji .

Mazauna garin sun ce jama'a sun fito daga gidajensu domin ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, sai dai har yanzu suna cikin zaman zulumi.

An yi ta barin wuta a garin, lamarin da ya sa mutane suka shiga cikin gidajensu domin su buya.

A safiyar ranar Talata ma, 'yan Boko Haram sun kashe mutane 17 a Damaturu babban birnin jihar ta Yobe.