Indiya za ta binciki safarar naman shanu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mabiya addinin Hindu, wadanda su ne daukacin kaso 80 cikin dari na al'umma biliyan 1.2 a kasar Indiya, kuma duk Shanu ne abin bautar su.

Kasar Indiya tana shirin kafa wani tsari na gwaji da na'urar zamani a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa domin bincika shiga da fitar naman shanu.

Hakan ya biyo bayan kashe wani Musulmi ne da aka yi kwanan baya saboda zargin yana cin naman shanun.

Yawancin jihohin kasar sun haramta cin naman shanu, duk da ana yarda da cin bauna.

Dokar haramta cin naman dai ta janyo cece-ku-ce a tsakanin al'umma, wadanda da dama daga cikin su ke bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin kasar da ta ke nema ta take hakkin su na cin abin da suke so.

Da yawa kuma sun ja hankalin gwamnatin cewar, naman shanu ya fi kaza da kifi araha, kuma yawancin al'ummar Musulmi da marasa galihu, wadanda ake kira Dalit, da kuma mutanen karkara na fama da talauci.

Karamin minista a ma'aikatar noman kasar, Sanjeev Kumar, ya shaidawa manema labarai cewa gwaje-gwajen za su tabbatar an duba duk naman da za a shiga da shi cikin kasar, kuma gwamnati za ta sa ido a kan lamarin.

Ya kara da cewa, "An yanke shawarar kafa na'urorin gwaji a tashoshin shigowa kasar saboda a dakile shigar naman shanu ba bisa doka ba".

Ya ce wannan doka za ta fi shafar yammacin birnin Mumbai ne, inda aka fi yawan safarar naman shanu.

Mabiya addinin Hindun kasar ne suka matsa lamba ga jam'iyyar da ke mulkin Indiya, Bharatiya Janata Party, da cewar su kara kaimi don ganin cewa an kare rayukan shanu a kasar.

A watan da ya gabata ne gungun wadansu mutane suka kashe Mohammad Akhlaq mai shekaru 50, a dalilin zargin shi da iyalansa da cin naman shanu, inda har suka raunata dansa wanda yanzu ke kwance cikin matsanancin hali a asibiti.

Duk da cewa an kafa dokar hana cin naman shanu a kasar, hukumar kula da nama ta Amurka ta bayar da rahoton cewa, Indiya ce ta fi kowa safarar naman bauna a duniya, inda ake zaton a shekarar 2015 ta fitar da tan miliyan biyu da dubu dari hudu, gaba da kasar Brazil wacce ta fitar da miliyan biyu.