'Yan majalisar India sun dambace kan naman shanu

Image caption 'Yan Hindu suna girmama shanu

'Yan siyasa na jam'iyyar BJP ta masu kishin addinin Hindu sun lakadawa wani dan majalisar dokokin yankin Kashmir duka bayan ya raba naman shanu a wajen wata liyafa da ya shirya.

Dan majalisar mai suna Rashid Ahmed wanda musulmi ne, ya jikkata kafin wasu 'yan majalisar na bangaren adawa suka ceto shi.

Mabiya addinin Hindu, wandada suke da rinjaye a India suna daukar saniya a matsayin abu mai tsarki da daukaka.

Cikin 'yan shekarun nan dai jihohi da dama sun tsaurara dokokin da ke haramta ciniki da cin naman shanu.

Wannan tasa an samu karuwar daukar tsauraran matakai a kan wadanda suke karya dokar.