Rasha ta yi wa IS barna a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rasha ta kai harin ne daga zango mai nisa

Rasha ta ce jiragen ruwan yakinta sun harba makamai masu linzami 26 a kan kungiyar IS a Syria, daga nisan daruruwan kilomita.

A wata hira ta talabijin da shugaba Putin, ministan tsaron kasar Sergei Shoigu, ya ce an yi nasarar lalata baki dayan wurare 11 da aka kai wa hari, kuma ba a taba fararan hula ba.

Mr Shoigu ya ce "nasarar da aka samu ta tabbatar da karfin makaman masu linzami daga nisan zango."

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan, kuma a baya kasashen yammaci sun soki Rasha a kan mara wa shugaba Assad baya a maimakon karya lagwan 'yan bindigar.

Yanzu haka kuma jami'an Syria sun ce dakarun gwamnati da taimakon jiragen yakin Rasha sun kaddamar da gagarumin farmaki a kan 'yan tawayen.