Rikicin Syria: Dalilin shigar Rasha

Image caption Shugaban Syria Bashar Assad.

Yayin da katsalandan din Rasha a yakin Syria ya ja hankulan hukumomin kasashen duniya, rayuwa dai ta ci gaba kamar yadda take a da a birnin Damascus da ke karkashin ikon gwamnati.

Har yanzu dauke wutar lantarki, da karancin ruwa, da kuma yunkurin kauce wa makaman roka ne manyan abubuwan da suka damu mazauna birnin.

Karar jiragen saman yaki na gwamnati da ke kai hare-hare ta riga ta zama jiki ga jama'a, saboda haka wannan abin da ke faruwa a baya-bayan nan ba wani abin daga hankali ba ne.

A cewar wata baiwar-Allah da ke zaune a birnin, Samar (ba sunanta na asali ba ke nan), ta waya, "Wa ya damu da ko waye ke kai hari kuma a ina; kusan duk kasashen duniya na da hannu a kashe-kashen da ake yi a Syria".

Shekaru biyar tun bayan fara zanga-zangar neman 'yanci da dimokuradiyya a Syria, har yanzu mutane a yankunan da ke karkashin ikon gwamnati na fargabar bayyana ra'ayoyinsu saboda tsoron jami'an tsaro za su tsare su.

Ga Samar, wannan katsalandan din da Rasha ta yi daidai ya ke da mamaye Syria, amma wadansu mutanen na ganin wani bangare ne na dadaddiyar alakar da ke tsakanin Rasha da Syria.

Dangantakar da ke tsakanin Damascus da Moscow ta kara karfi ne bayan mahaifin Bashar al-Assad, Hafez, ya kulla kawancen soji da tsohuwar Tarayyar Soviet.

"Tun zamanin Tarayyar Soviet, Rasha ta ke kara yaukaka dangantakar ta da Syria", a cewar wani mawaki da ke zaune a birnin Damascus, wanda wani dan Rasha ya koyar da shi ya bayyana.

'Karatu a Rasha'

Hadin gwiwa tsakanin Syria da Rasha ya dauki siffofi daban-daban: mafi muhimmanci shi ne ta fuskar soji, amma kuma a wadansu matakan, an baiwa kamfanonin Rasha kontiragi mai tsoka a bangaren man fetur da iskar gas da kuma wasu masanantu.

Tasirin Rasha ya bayyana har ma a tsarin gine-gine na Damascus. A kan babban titin zuwa Homs, an gina wadansu rukunonin gidaje ga kwararru 'yan Rasha da iyalansu, wadanda aka kwaikwayi tsarinsu a wadansu gine-ginen a sassa daban-daban na birnin.

Cibiyar Raya Al'adun Rasha da ke birnin Damascus wuri ne da a da 'yan Syria ke zuwa su koyi al'adun Rasha, har ma su koyi raye-rayensu kuma su sha barasar Vodka.

An bai wa 'yan Syria tallafi da kuma guraben karo ilimi su je su yi karatu a Rasha. Galibin wadannan mutane suna da alaka da gwamnati da jam'iyyar Ba'ath mai mulki.

Yawancinsu dai sun dawo da takardun sheda na bogi an kuma nada su a manyan mukamai a gwamnati da fannin ilimi.

'Babu Mulki'

Sai dai Dokta Salwa Abed Allah, wacce ta yi karatu a Rasha, ba haka ta ke kallon abubuwa ba.

A cewar ta, "Akwai wadansu kungiyoyi da jam'iyyu da suka aika dalibai su yi karatu amma suka dawo ba komai, amma yawancin daliban da gwamanti ta tura sun dawo da kyakkyawar shaidar karatun."

Ga Dokta Abed Allah, katsaladan din da Rasha ta yi na baya-bayan nan abu ne da ake maraba da shi, kuma tana fatan hakan zai kawo karshen yakin Syria.

"Ba ma so mu ga sojojin kasashen waje a kasarmu, amma kuma idan har aka ba mu zabi tsakanin kungiyar IS da Rasha, to tabbas muna maraba da Rasha".