Ameachi: Kan sanatoci ya rabu

Hakkin mallakar hoto Amaechi Twitter
Image caption Amaechi yana fuskantar barazana daga cikin gida

Kan sanatoci ya rabu a majalisar dattawan Najeriya bayan da wasu 'yan majalisar daga jihar Rivers da ke kudu maso kudancin kasar suka gabatar da takardar koke domin neman majalisar kada ta tantance tsohon gwamnan jihar, Mt Rotimi Ameachi a matsayin minista.

Hakan dai ya haddasa rudani a zauren majalisar tsakanin wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki da kuma 'yan jam'iyyar adawa ta PDP dangane da amince wa da takardar koken.

'yan jam'iyyar dai ta APC na cewa ba a bi ka'ida ba wajen mika takardar koken, lamarin da suka ce ba zai yi wani tasiri ba.

'Yan Najeriya dai na dakon ranar 13 ga watan Octoba, ranar da shugaban majalisar dattawan kasar ya ce za su fara tantance jerin sunayen ministocin da shugaba Buhari ya aike wa da majalisar domin tantancewa.