Kotu ta amince wa Kagame ya yi tazarce

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kagame yana son yin ta-zarce.

Kotun Kolin Rwanda ta amince a gyara kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa Shugaba Paul Kagame damar neman wa'adin mulki a karo na uku.

Jam'iyyar hamayyar kasar ta Green Party ce ta kai kara a gaban kotun domin a hana shugaban ci gaba da mulki, sai dai kotun ta bukatar ba ta da tushe.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato Alkalin Alkalan kasar, Sam Rugege, yana cewa, "Bukatar da 'yan hamayyar suka gabatar mana ba ta da tushe, don haka an kori karar da suka shigar."

A watan Yuli ne 'yan majalisar dokokin kasar suka amince su gyara kundin tsarin mulkin, sannan a gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da bukatar shugaban kasar ta yin ta-zarce.