Mako guda babu Ebola a Afrika

Hakkin mallakar hoto

Kasashen yamancin Afrika guda uku wadanda suke inda Ebola ta yi kamari, sun yi mako guda cir babu wani wanda ya kamu da cutar tun barkewar ta a watan Mayun shekarar 2014.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, ya zuwa yanzu,c utar ta kashe sama da mutane 11,000 a Guinea da Liberiya da Saliyo.

Kamuwa da cutar ta ragu sosai a shekarar 2015, amma kuma hukumar lafiyar ta duniya ta yi gargadin cewar cutar za ta kuma iya barkewa.

Annobar ita ce barkewar cutar Ebola mafi muni a tarihi.

'Mutane 500 a Guinea'

A wani rahoto da WHO din ta fitar ta ce a Guinea ana duba lafiyar sama da mutane 500 wadanda ake ganin sun samu alaka mai daga hankali da masu cutar Ebolan a kai a kai.

Hukumar ta kuma ce mutane da dama wadanda ke da hadari sosai na kamuwa da cutar wadanda suke da alaka da masu cutar Ebolan a Guinea da kuma Saliyo, ba a san inda suke ba.

An riga an ayyana Liberia a matsayin kasar da bata da masu cutar Ebola bayan ta shafe kwanaki 40 babu wani wanda ya kamu da cutar.

Wannan shi ne karo n biyu da aka bayyana kasar da wannan matsayi bayan barkewar cutar a watan Yunin bara.

Saliyo ta bayyana mutum na karshe na kasarta mai cutar ne a ashirin da takwas ga watan Satumba amma kuma yanzu dole ta jira a bayyana ta a matsayin kasar da ba ta da masu cutar Ebola.

Guinea ta bayyana wadanda suka kamu da cutar Ebola na baya bayan nan ne a 27 ga watan Satumba.