An kashe masu bikin aure 13 a Yemen

Image caption Ana zargin jiragen saman Saudiyya da hannu wajen kai harin.

Rahotanni daga kasar Yemen sun ce an kashe mutane a kalla 13 da ke wani wajen bikin daurin aure a hare-hare ta sama da aka kai musu.

Lamarin ya faru ne a garin Sanban mai nisan kusan kilomita 100 daga Sanaa, babban birnin kasar, wanda ke hannun 'yan tawaye.

Ganau sun ce jiragen da suka kai harin suna sane cewa a wajen ake bikin da wani shugaban da ke goyon bayan kungiyar 'yan tawaye ta Houthi ke jagoranta.

Sun kara da cewa jiragen saman yakin da Saudiyya ke jaroganta -- wadanda ke goyon bayan Shugaba Abedrabbo Mansour Haddi -- ne suka kai harin.