Hayatou ya zama shugaban riko na Fifa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Issa Hayatou ya zama mai rikon kwaryar Shugaban Hukumar kwallon kafa ta FIFA.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta bayyana Issa Hayatou, a matsayin shugabanta na rikon kwarya.

Tun da aka kaddamar da hukumar shekaru sama da 111, wannan ne karon farko da jagoran Fifa ya fito daga Afrika.

Hukumar kwallon kafa ta dakatar da tsohon shugabanta, Sepp Blatter, har kwanaki 90, hakan kuma ya sanya aka maye gurbin sa da Issa Hayatou, wanda shi ne mataimakin shugaban hukumar da ya fi girma.

Issa Hayatou, haifaffan kasar Kamaru ne, kuma dan sarki, inda wasu cikin 'yan uwansa ke siyasa har ma dan uwansa ya yi Firayi Ministan Kamaru a baya.