'Yan majalisar dokokin Libya na nuna shakku kan MDD

Wakilan majalisun dokoki masu hamayya da juna a Libya sun bayyana shakkunsu game da shawarar da majalisar dinkin duniya ta bayar ta nema kafa gwamnatin hadin kan kasar.

Wakilin majalisar dinkin duniya, Bernardino Leon, ya sanar da shirin ne a ranar Alhamis bayan an shafe kusan shekara ana tattaunawa tsakanin 'yan majalisa masu goyon bayan majalisar kasar wadanda suke Tripoli, babban birnin kasar da gwamnatin da ke gabashin kasar, wacce kasashen duniya ke mara wa baya.

Yanzu dole ne majalisun biyu su kada kuri'a a kan yarjejeniyar, amma kuma da dama daga cikin 'yan majalisar suna ganin lokaci bai yi ba na kafa gwamnatin hadin kan kasar.

Shi ma Mr Leon ya amince yin hakan zai fi wahala a kan yin yarjejeniyar.

Amma kuma ya ce, a kalla yin hakan zai samar da kwanciya hankali kuma 'yan kasar Libya da dama sun riga

sun rasa rayukansu.