'An tabbatar babu cutar Ebola a Nigeria'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane a jihar Calabar sun shiga cikin zullumi

Hukumomin a Nigeria sun tabbatar da cewa babu cutar Ebola a cikin kasar, bayan da aka nuna fargaba game da yiwuwar bullar cutar a jihar Calabar da ke kudancin kasar.

Babban jami'i a ma'aikatar lafiyar kasar, Dr Nasiru Sani Gwarzo shi ne ya tabbatar wa BBC hakan a hira ta wayar tarho.

A cewarsa, sakamakon gwajin da aka gudanar a kan wani matashi da ya rasu jim kadan bayan da aka kwantar da shi a asibiti, ya nuna cewar ba Ebola ba ce ta kashe shi.

Matashin ya rasu ne jim kadan bayan da aka kwantar da shi a asibiti sakamakon wata cutar mai alamomi kamar Ebola.

A ranar Laraba, hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa kasashe uku da cutar Ebola ta fi yi wa illa watau Guinea da Saliyo da kuma Liberia -- sun shafe mako guda na farko ba tare da samun wani da ya kamu da cutar ba tun bayan bullar cutar a shekarar 2014.