An kai harin roka a kudancim Israila

Falasdinawa masu zanga-zanga Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Falasdinawa masu zanga-zanga

Sojojin Isra'ila sun ce mayakan sa-kai na Palasdinu a zirin Gaza sun kaddamar da wani harin roka akan kudancin Isra'ilar, 'yan sa'o'i bayan da wasu sojojin kasar suka kashe palasdinawa guda shida a kan iyakar kasashen biyu.

Sai dai dakarun Isra'ilar sun ce rokar da aka harba ta sauka ne a wani fili, al'amarin da ya ankarar da al'ummar yankin harma aka fara busa jiniyar da ake yi idan wani abun hadari ya faru.

A ranar Juma'a ne dai, rundunar sojin ta Isra'ila ta ce dakarunta sun bude wuta a kan iyakar Palasdinu domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga dake jifan sojojinta tare da kona tayoyi.

Sai dai shugaban kungiyar fafitikar nema wa Palasdinawa 'yanci ta Hamas, Isma'il Haniya ya ce alamu na nuna cewa wani sabon tashin hankali zai barke nan ba da dade wa ba.