Turkiya: Harin bam ya hallaka mutane 86

Image caption A kalla mutane 86 ne suka mutu a harin bam na Turkiya

Wasu bama bama biyu da suka fashe a wani taron gangamin zaman lafiya a tsakiyar Ankara babban birnin Turkiya ya kashe mutane a kalla 86, wasu kimanin 200 kuma sun sami raunuka.

Wani hoton bidiyo ya nuna masu taron gangamin sun rike hannayen juna suna maci tare da rera wakoki lokacin da bam din ya fashe.

An shirya machin ne don neman gwamnati ta dakatar da hare-haren don neman gwamnatin Turkiya ta daskatar da hare-haren da take kai wa kan mayakan sa kai na Kurdawa.

Gwamnati na zargi masu tayar da kayar baya da kai hare-haren, yayin da shi kuwa jagoran jam'iyyar HDP mai goyon bayan Kurdawa yake zargin gwamnatin kasar da shirya kai harin.

Ana zargin dan kunar bakin wake ne ya kai daya daga cikin hare-haren.