Rundunar Sojin Nigeria ta gargadi Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta ce Boko Haram na dab da zuwa karshe.

Rundunar sojin Najeriya ta sake yin gargadi ga mayakan Boko Haram da su gaggauta mika wuya kafin dakarun sojin kasar su murkushe su.

Kakakin rundunar Sojin kasar ya fitar da sanarwar, wacce aka yi wa lakabi 'gargadi karo na biyu'.

Sanarwar gargadin ta bukaci duk wani ko wasu 'yan kasar da ke da alaka da mayakan Boko Haram da su gaggauta ba su shawarar ajiye makamansu kafin lokaci ya kure musu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa rundunar ta gano sansanonin 'yan boko Haram da sauran wuraren da suke buya kuma a shirye take ta murkushe su idan har ba su mika wuya ba.

Mayakan kungiyar Boko Haram 200 dai sun mika wuya a garin Geidam a kwanakin baya.