Syria: An zargi Kurdawa da aikata laifuka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amnesty International ta bukaci kasashen yammacin duniya su daina rufe ido idan Kurdawa suna aikata laifuka.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mayakan Kurdawa a Syria da laifin tilasta wa dubban mutane ficewa daga gidajensu daga yankunan da suka kwato daga hannun 'yan kungiyar IS mai ikirarin kishin Musulinci.

Kungiyar ta ce yawancin mutanen da Kudawan suka kora daga gidajensu Larabawa ne.

Ta kara da cewa Kurdawan sun lalata yawancin kauyukan da ke arewa maso gabashin Syria.

Kungiyar ta bukaci kasashen yammacin duniya da kada su yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Kurdawan, wadanda kawayensu ne.

Jiragen yakin Amurka dai sun fara bai wa Kurdawan makamai domin taimaka musu wajen yakin da IS.