Ciyar da yaran da ta'adancin BH ya shafa

Hakkin mallakar hoto Mark Naftalin

Wasu yara maza wadanda hare-haren kungiyar Boko Haram suka tursasawa barin gidajensu sun samawa kansu mafaka a wani gidan Biredi a Najeriya.

'Yan'yan masu gasa biredi ne wadanda 'yan kungiyar Boko Haram suka kashe ko suka yi garkuwa da su wadanda wani ya hado kansu.

"Ka ji labarin mai gidan biredi da mutanen da suka rasa muhallansu?"

Na zaci zolaya ta abokina dan Najeriya yake yi da ya yi mini wannan tambayar. A lokacin muna dan hutawa ne a wani otel a Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda hare-haren Boko Haram suka yi kamari.

Sai dai ba wasa ya ke ba. Ya ji labarin wani gidan biredi da ya zama wurin fakewa ga mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

Nemo wurin bai yi min wahala ba. Maiduguri, babban birnin jihar Borno, na da girma sosai, kuma a lokacin ba ni da wani cikakken kwatancen gidan biredin.

Da na isa inda na ke zato nan ne, ban ga gine-ginen da suka yi kama da gidan biredi ba.

Babu wata alama ko ma buhunhunan fulawa. Hayakin motoci daga tituna ya mamaye duk wani kanshin biredi da aka gasa.

Hakkin mallakar hoto Mark Naftalin

Amma kuma kwatsam sai na gan shi - wani gini mai bangon tsohon kwano da ya yi tsatsa kuma a saman ginin akwai wurin da hayaki ke dan fita, da alamar ana gasa wani abu.

Da na shiga ciki, sai mai gidan biredin ya matso, ya dora hannayensa a dunkule a kan kirjinsa, alamar gaisuwa ta al'adarsu, gaisuwa ta mutunci.

Mutumin dogo ne, zai haura shekaru 50 da haihuwa kuma ya yi shiga ta mutunci, inda ya saka doguwar riga wacce ta kai masa gwiwarsa da kuma dogon wando wanda bai kama jiki ba - ranar Juma'a ce saboda haka a lokacin bai dade da dawowa daga masallaci ba.

Shi ma gidan biredin a kintse ya ke - gidan biredin yana da daki daya wanda aka yi wa dabe da siminti da kuma murhun gasa biredi na gargajiya a loko.

Ashe tsammanin da na yi ban yi dai dai ba - ashe babu abin da ake gasawa.

Wutar ma ta kusa mutuwa. An gama gasa biredin ranar. An tara biredin sayarwa da aka daddaure da yawa a kan tebur.

A can karshen dakin, na ga yara maza da dama a kan tabarma a kasa. An shaida min cewar karamin cikinsu shekarunsa takwas sannan babban cikinsu shekarunsa 16.

Wasu daga cikin kananan yaran suka dan yi murmushi kuma su ma suka dago min hannayensu kamar yadda na yi musu.

Ni da mai gidan biredin muka zauna a kan kujera a kusa da tukubar gasa biredin. Zafi yana fitowa daga jikin kujerar. Da taimakon tafinta, ya yi min bayanin cewar yaran duka sun zo nan ne bayan kungiyar Boko Haram ta kai hari gidajensu.

'Ya'yan wasu masu gidan biredi ne daga wasu kauyukan da ke wajen Maiduguri. Mahaifansu suna cikin dubbai da aka kashe ko aka yi garkuwa da su sakamakon ta'addanci.

Hakkin mallakar hoto Mark Naftalin

Sun fara isowa nan ne a shekarar 2012 - da farko mutane kadan ne amma a shekarar da ta wuce, Boko Haram ta zafafa kai hare-harensu a cikin da kewayen Maiduguri.

Ya ce ya taimaka wajen bai wa mutane kusan 300 muhalli, yawancinsu mata da yara.

Yan Najeriya sama da miliyan biyu sun rasa muhallansu a shekaru hudu da aka shafe ana fada.

Kadan daga ciki ne, wato kashi goma a cikin dari, suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira na gwamnati. Mafi yawansu suna dogaro ne da abokai da 'yan uwa ko mutane masu kirki wadanda ba su sani ba.

Amma taimakonsa na da iyaka - yadda yanayin wurin nasa ya ke ya bayyana alamun hakan. Ba abin da zai iya baiwa wadannan yara matasa illa wannan dakin kwanciya da kuma biredin da za su rika ci kullum.

Hakkin mallakar hoto Mark Naftalin

"Kana fada?" na tamabayi wani yaro mai shekaru 15 wanda ya shafe tsawon shekaru biyu a wurin. Sai ya yi dariya ya gyada kansa amma kuma sai ya ce yana kokari ya shige dakin da wuri saboda ya kebe a lokon da yafi so ya kwanta a kusa da taga.

Na tambaye su a kan makaranta. Sai ya girgiza kafada ya ce min bai je makaranta ba tun da ya zo nan.

Amma kuma yana so ya koma, da zarar ya koma gida. Ya ce yana so ya yi karatu ya zama wani babban jami'in gwamnati.

A yanzu dai yana fatan cika wannan burin a wannan karamin muhalli da 'yan kalaman Turanci da kuma kirkin mai gidan biredi.

Hakkin mallakar hoto Mark Naftalin