Yan adawar Guinea sun yi kiran sake zabe

Yan takarar shugabancin kasa a Guinea
Image caption Yan takarar shugabancin kasa a Guinea

Shugaban 'yan adawar Celllou Dalein Diallo yana magana ne a madadin baki dayan 'yan takarar shugaban kasar bakwai da suka fafata da shugaba mai ci, Alpha Conde.

Hukumar zaben kasar ta Guinea ta ce sai karshen wannan mako zata bayyana sakamakon zaban.

An kashe mutane da dama a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan gwamnati da na 'yan adawa lokacin yakin neman zaban.

Jam'iyyar dake mulkin ta yi watsi da zargin magudin.

Wannan shine karo na biyu da aka yi zaben da ya kunshi jam'iyyu da dama tun bayan da kasar ta sami yancin kai a shekarar 1958.