PDP ta yi sakaci a kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu 'yan jam'iyyar PDP sun ce Goodluck Jonathan bai dauki mataki kan Boko Haram da wuri ba.

Wasu shugabanni a babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Nigeria sun ce sakacin da jam'iyyar ta yi wajen tunkarar matsalar Boko Haram a shekaru 16 da jam'iyyar ta kwashe tana mulki a kasar, ya taimaka wajen ta'azzara matsalar.

Mataimakin Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar PDP, Barrister Abdullahi Jallo, ya ce tuntuni suke fadawa shugabanninsu cewa ya kamata a dauki kwakwaran matakin magance Boko Haram, amma hakan bai yiwu ba.

Ya yaba da irin matakan da Shugaba Muhammadu Buhari ke dauka na magance hare-haren Boko Haram.

Barrister Jallo ya ce, "Babu wani dan PDP da zai ce ba ya so a murkushe Boko Haram, amma da shugaba Jonathan ya yi abin da shugaba Buhari ke yi yanzu, da ba a sha wahala haka ba."

Ya kuma bayyana goyon bayan jam'iyyar PDP kan matakan da kungiyar gwamnonin arewacin kasar suka dauka na kaddamar da wani kwamiti na musamman domin yi wa dokokin jihohinsu garambawul, a wani mataki na shawo kan matsalar ta Boko Haram.